AminuBagudo

Journalist : Editor In Chief At Pejoweb.com

Articles
31
Followers
6

profile/22FB_IMG_16047646168385907.jpg
AminuBagudo
Shugaba Buhari Ya Tura Wakilansa Zuwa Daurin Auren Dan Gwamna A Najeriya
~1.8 mins read
Shugaba Buhari ya tura ministan yan sanda da wasu manyan jami'ai don su wakilce shi a wajen bikin dan Gwamna Tambuwal
- Najib dan Gwamna Tambuwal na Jihar Sokoto ya auri Amina Tafida yar Sanata Umar Tafida
- Shugaban kasar ya shawarci ma'auratan da su zauna lafiya su kuma girmama juna
Shugaba Muhammadu Buhari ya amsa gayyatar auren Najib Aminu Waziri, dan gidan Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ranar Asabar 15 ga watan Nuwamban shekarar 2020.
Najib ya auri Amina Umar Tafida, yar gidan Sanata Umar Tafida, Tafidan Argungu, a wani shagali da akayi a Argungu, Jihar Kebbi kamar yadda Daily Trust ya ruwaito.
Buhari ya tura wakilci bikin dan Tambuwal

Buhari ya tura wakilci bikin dan Tambuwal. Hoto: @daily_trust

Shugaba Buhari ya samu wakilcin ministan harkokin yan sanda, Alhaji Maigari Dingyadi, Ministan Shari'a Abubakar Malami da babban mai taimaka masa bangaren yada labarai Malam Garba Shehu, da Musa Haro ma'aikacin fadar shugaban kasa.
Shugaban kasa, a jawabin da ya yi ta bakin mai kakakinsa Malam Garba Shehu, ya shawarci ma'auratan da su ji tsoron Allah su girmama juna.
"Ina shawartarku da ku zauna lafiya, kada ku gaji da juna," a cewar sa.
Shugaban ya kuma taya gwamnan Sokoto murnar shagalin kuma ya yi fatan a kare taron lafiya.
A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, wasu magidanta a karamar hukumar Ganjuwa ta Jihar Bauchi sun koka kan karancin kororon roba a yankin wadda ke taimaka musu wurin bada tazarar haihuwa.
The Punch ta ruwaito cewa shugaban kwamitin Cibiyar Lafiya ta mazabar Kafin Madaki, Mustapha Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da ya yi wa manema labarai jawabi.
"Mu a matsayinmu na kwamiti, mun dukufa wurin wayar da kan al'umma kuma da dama cikinsu sun rungumi wannan tsarin sosai.
"Maza a yanzu suna fitowa fili su nemi a kawo musu kororon roba don su taimakawa matansu, sai dai a halin yanzu wadanda muke da su nan sun kare," a cewarsa
profile/22FB_IMG_16047646168385907.jpg
AminuBagudo
Wasu 'Yan Najeriya Sun Amince 'Yan Boko Haram Ne Saboda Azabtarwa
~47.4 mins read

IIyalan wasu ’yan Najeriya da aka yanke wa hukunci kan zargin alaka da kungiyar Boko Haram sun ce su aka yi suka amsa laifin da ba su aikata ba.

Wata kotu a HadaddiyIar Daular Larabawa (UAE) ce ta yanke wa ’yan Najeriyan hukuncin da ’yan uwan nasu ke ganin babu adalci.
  • Dubai ta daure ‘yan Najeriya 6 kan ‘daukar nauyin’ Boko Haram
  • An cafke shi da katin ATM 5,000 a hanyar Dubai
  • Boko Haram: Sojoji na neman mutum 81 ruwa a jallo
  • Za a iya magance rikicin Boko Haram a siyasance – Zulum
  • Yusuf Ali Yusuf dan uwan Ibrahim Ali Hassan da Bashir Ali Yusuf wadanda kotun ta yanke wa hukuncin daurin shekaru 10 ya shaida wa wakilinmu cewa, “Ibrahim yana harkar canjin kudi kuma yana da rajista da hukumar Dubai.

    “Yana kasuwaci da mutane da dama sannan yana ajiyar kudaden mutane, wanda daga ciki yana tura kudi Hong Kong, China da sauransu”.
    Yusuf ya kara da cewa an tursasa daya daga cikin ’yan Najeriyan da ake zargi mai suna Surajo ne ya amsa laifin da bai aikata ba, aka kuma yi masa romon-baka cewa ya nuna abokan huldarsa.
    Ta haka ne, a cewarsa, aka kama Ibrahim da Bashir, aka azabtar da su, aka tursasa su amsa laifin da ya sa kotun ta daure su shekara goma-goma.
    Dadewarsu a tsare
    Yusuf ya bayyana wa wakilinmu cewa, “An kama su a Afrilun 2017 sannan suka shafe shekara daya da rabi kafin daga baya aka fara shari’a.
    “Sun shafe wata shida a hannun hukumar farin kaya ta SSS sannan suka yi zaman wakafi na shekara daya a gidan yari”, inji Yusuf.
    Ya ce a zaman kotun an ki ba su damar yin magana ballantana su kare kansu daga tuhumar da ake musu.
    A cewarsa, Surajo da Saleh kadai aka ba damar magana a kotun; a zaman farko Surajo bai ce komai ba sai a zama na gaba ya shaida wa kotun cewa tursasa shi jami’an tsaro suka yi, amma duk da haka kotun ya yanke hukunci.
    Tsakanin iyalansu da gwamantin Najeriya
    Ya ce tun da aka fara shari’ar suke fafutukar ganin hukumomi masu alhaki a Najeriya sun bibiyi lamarin don tabbatar da anyi wa ’yan uwan nasu adalci.
    Kamar yadda ya ce, Sun je Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje, sun sha ganawa da tsohuwar Minista a Ma’aikatar, Khadija Bukar Abba Ibrahim a wancan lokaci, ta kuma ba su tabbacin gwamnati za ta yi duk abin da ya dace na ganin an sake su.
    Ya ce sun kuma gana da Ministan Shari’a Abubakar Malami a kan lamarin, ya ba su tabbacin yin iya bakin kokarinsa, amma daga baya sai ta kasance ba sa samun ganin sa idan suka je ofishinsa a kan batun.
    Daga bisani suka kai koke Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osibanjo, inda aka ba su kwarin gwiwar za a yi kokarin ganin komai ya kammala cikin ruwan sanyi.
    Da aka tuntubeshi, Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya shaida wa manema labarai cewa ofishinsa na da masaniya a kan lamarin.
    Malami ya ce sun tura wa hukumomin Dubai bukatar a turo wa Najeriya kundin binciken da shari’ar da aka gudanar kan ’yan Najeriyan.
    Amma shiru (UAE) ba ta turo wa gwamnatin Najeriya sakamakon binciken nasu ba.
    Mahangar jama’a
    Ammar Aminu ya yi zargin sakacin gwamnati ne ke sa ake wa ’yan Najeriya mazauna kasashen waje kazafi a kuma hukunta su a kai.
    “An dade ana yanke wa ’yan Najeriya hukucin sharri saboda rashin gatansu, wanda mafi yawa daga cikinsu ba su aikata laifin da ake tuhumarsu da shi ba”, cewarsa.
    Ibrahim Aliyu Usman (Shanee) dan canji a kasuwar Wapa da ke Kano, na shakkar cewa wadanda aka yanke wa hukuncin za su aikata abin da ake zargin su.
    “Na zauna da su tsawon shekaru muna huldar kasuwanci, mutane ne masu rikon amana da gaskiya, babu abin da zai sa su aikata laifi makamancin wannan”, inji Shanee.
    Mubarak Mustapha kuma cewa ya yi wannan batu ne da ke bukatar bincike na tsanaki saboda ya shafi ta’addanci.
    A nasa bangaren, Usman Usman na ganin idan har an tabbatar suna da alaka da ’yan Boko Haram to hukuncin da aka yanke ya yi.
    Wasu kuma na ganin in har gaskiya ake nema, to abin da ya fi dacewa shi ne a dawo da su Najeriya a ci gaba da shari’ar saboda a nan ake rikicin Boko Haram ba a Dubai ba.
    Fahimtar lauyoyi
    Barista Habibu Ma’aruf, lauyan Ibrahim da Bashir, ya ce sakacin gwamnati ne ke jefa ’yan Najeriyan cikin tsaka mai wuya a kasashen waje.
    “Dubai ba ta yi adalci ba domin wanda ake zargin ba a ba su damar yin bayani ba, ballantana damar gabatar da shaidu.
    “Kotun ba ta bayar da wasu dalilai da suka nuna suna mu’amala da ’yan Boko Haram ba.
    “Amma gwamnatin Najeriya za ta iya bin hanyar diflomasiyya wurin warware wannan lamari”, cewar Barista Ma’aruf.
    Ya ce dole ne gwamnatin Najeriya ta rika ba ’yan kasarta mazauna ko ’yan kasuwa a kasashen ketare kariya daga hukucin da ake yanke musu ba bisa hakki ba.
    “Dole sai gwamnati ta ba wa ’yan Najeriya da ke kasashen waje kariya, saboda irin wannan ya faru da wata yarinya a kasar Saudiyya”, inji shi.
    Barista Bulama Bukarti
    Barista Bulama Bukarti lauya ne mai zaman kansa kuma mai bincike a kan ayyukan Boko Haram a Najeriya, ya ce akwai lauje cikin nadi game da shari’ar.
    “Tun da na karanta wannan labari zuciyata ke min kaikayi a kan wasu abubuawa.
    “An ce wadannan mutane suna tura wa wakilan Boko Haram kudi ne a Najeriya.
    “Amma kuma ta tabbata cewa ita Hadaddiyar Daular Larabawa ba ta hada kai da gwamnatin Najeriya wajen yin bincike tare da gano su wa ake tura wa kudin ba”, inji Bukarki.
    Ya kara da cewa ko da gwamnatin Najeriya ta gamsu da hukuncin da aka yanke, yana da kyau ita ma ta yi nata binciken domin tabbatar da gaskiyar lamarin.
    Idan kuma ta gano ba a yi wa ’yan kasarta adalci ba, sai ta kwatar musu hakkinsu ta hanyar diflomasiyya.
    Masu sharhi na ganin gwamnanti na bukatar ta sa ido kan yadda ake tauye hakkin ’yan Najeriya ba bisa ka’ida ba a kasashen ketare da sunan hukunci.
    Rashin hakan ke kai wa a daure ’yan kasar ko a zartar musu da hukuncin kisa a kasashen waje saboda laifukan da ba su aikata ba.
    Tunda lamari ne da ya shafi ta’addanci, babba ne, kuma tsaron al’ummar kasa, Najeriya na bukatar ta ba da muhimmanci ga harkar bincike da hukunta masu laifi da kuma tabbatar da adalci ga wadanda ake zargi.
    Kar a koma ‘yar gidan jiya
    A irin hukunci da ake yankewa ’yan Najeriya a ketare ne a 2019 aka kusa kashe wata daliba a Jami’ar Yusuf  Maitama Sule da ke Kano, Zainab Habib Aliyu.
    Bayan Saudiyya ta yanke wa Zainab hukuncin kisa bisa zargin safarar kwayoyi ne matasa suka yi zanga-zangar lumanar goyon bayanta da jan hankalin gwamnati ta bibiyi lamarin.
    Najeriya ta kafa kwamitin da ya kai ga tseratar da dalibar bayan zurfafa bincike da ya gano cewa wasu ma’aikatan filin jiragi na Malam Aminu Kano ne suka sa kwayoyi a cikin kayanta a hanyarta ta zuwa Saudiyya yin Umrah.
    Don haka wasu ke ganin shi ma hukunci da aka yanke wa wadannan ’yan Najeriya a UAE bisa zargin tura kudi domin taimaka wa Boko Haram a Najeriya, ba mamaki irin abin da ya nemi ritsawa da Zainab ne.
     

    An Yankewa ‘Yan Fashi Biyu Hukuncin Kisa A Ekiti

    NOVEMBER 12, 2020 AT 5:15:32 PM
     
    SANI IBRAHIM PAKI

    Wata babbar kotun jihar da ke zamanta a Ado-Ekiti babban birnin jihar Ekiti a ranar Laraba ta yankewa wasu mutane biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda fashi da makami.

    Wadanda aka yankewa hukuncin, Lanre Kayode mai shekaru 34 da Olanrewaju Aremu mai shekaru 35, wadanda suke dauke da bindigogi da adduna, sun yi wa wata mata mai suna Oluremi Jimoh fashin na’ura mai kwakwalwa, wayoyi da mota kirar Toyota Camry.
  • Fitaccen mai yaki da ‘yan fashi, Ali Kwara ya rasu
  • ’Yan sanda sun bindige dan fashi a Katsina
  • Hukuncin dai ya zo ne kasa da mako guda bayan da wata Babbar Kotun Jihar ta yanke wa wasu maza biyu hukuncin kisa kan irin makamancin wannan laifin.
    Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, mai shari’a Lucas Ogundana ya ce, hukuncin ya yi daidai da tanadin doka kan duk wanda aka tabbatar ya aikata laifin.
    Tun da farko dai an tuhumi mutane biyun ne da amfani da bindigogi da adduna don yi wa wata mata mai suna Jimoh Folajoke Oluremi fashin kayan da suka hada da na’ura mai kwakwalwa da wayoyi da kuma motar a ranar 14 ga watan Yulin 2017, da misalin karfe biyu na dare a unguwar Oke-Ila dake Ado-Ikiti,
    Matar ta shaidawa kotun cewa an kama wadanda ake zargin ne bayan yan sanda sun bibiyi wayoyinta bayan aikata fashin, wanda hakan ya sa aka kwato sauran kayayyakin.
    Tun da farko dai Babban Mai Shigar da Kara na jihar Olawale Fapohunda ne ya shigar da karar ya kuma gabatar da shaidu hudu, kafin daga bisani su ma wadanda ake zargin su amsa aikata laifin da kansu.

     

    Jirgin Soji Ya Yi Hatsari A Kasar Masar

    NOVEMBER 12, 2020 AT 4:37:15 PM
     
    SAGIR KANO SALEH

    Wani jirgin soji ya yi hatsari a kasar Masar inda ya kashe mutu bakwai da ake cikinsa.

    Helikwaftan ya rikito ne a yankin Sinai na kasar Masar a lokacin da yake dauke da sojoji da masu aikin sa ido na hadin gwiwa.
  • Tsohon Shugaban Ghana Jerry Rawlings ya rasu
  • Sojin Larabawa sun kakkabo jiragen ’yan Houthi a Saudiyya
  • Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce wadanda suka mutun sun hada da Amurkawa biyar, Bafaranshe daya da kuma dan Jamhuriyar Czech.
    Wata majiya a Isra’ila ta ce jami’an da hatsarin ya ritsa da na daga cikin rundunar wanzar da zaman lafiya da aka kafa tun a 1979.
    Ta ce an kafa rundunar ce a lokacin da aka kulla yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Masar kuma ba ta da alaka da Majalisar Dinkin Duniya.

    Garken Giwaye
     

    Giwaye Na Barazana Ga Noman Abinci A Borno

    NOVEMBER 12, 2020 AT 3:57:29 PM
     
    ABUBAKAR MUHAMMAD USMAN

    Wani garken giwaye na barazana ga noman abinci a garin Kala-Balge da ke Jihar Borno.

    Giwayen kusan 250 sun tsallako daga kasar Chadi suka ratso ta Kamaru, sannan suka fara rayuwa a garin Kala-Balge.
  • Sojoji sun bindige ’yan Boko Haram 22 a Borno
  • ‘Yan Boko Haram 16 da ‘yan gudun hijira 4 sun mutu a musayar wuta a Borno
  • ’Yan Boko Haram sun kashe manoma 8 a Borno
  • Boko Haram: An umarci ‘yan jihar Borno su yi azumi ranar Litinin
  • Babagana Shettima wanda shugaba ne a Kala-Balge, ya ce, “Mutane suna cikin wahala, da yawansu suna zaune ne a sansanin ‘yan gudun hijira.
    “Dole ne su yi noma domin su samu abin da za su ci amma giwaye sun cika gonakin da suke noman”, inji shi.
    Akalla mutum 8,000 ne daga Kala-Balge ke ci gaba da zama a sansanin ‘yan gudun hijira saboda gudun ta’addacin ‘yan Boko Haram.
    Shettima ya kara da cewa sai mutanen Kala-Balge sun yi tafiyar mil 12 a kullum zuwa iyakar Kamaru domin sayen abinci.
    Hare-haren Boko Haram ya sa giwaye ya da zango yankin domin ci gaba da rayuwa.
    Kafin watan Oktoba, an yi hasashen akwai giwaye 300 dake rayuwa a dazuka daban-daban a fadin Najeriya.
    Hare-haren Boko Haram a yankin Tafkin Chadi ya tilasta wa mutane sama da miliyan biyu yin hijira daga gidajensu domin tsira da rayuwarsu.

     

    Kotu Ta Umarci A Biya Masu Zanga-Zangar Da Aka Kashe Diyyar N1.1bn

    NOVEMBER 12, 2020 AT 3:05:54 PM
     
    SANI IBRAHIM PAKI

    Wata kotun Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta sami kasar Gini da laifin kisan masu zanga-zanga a kasarta a shekarar 2012 tare da umartarta ta biya su diyyar N1,159,740,000.

    Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa kotun ta ba kasar watanni shida domin ta biya diyyar da yawanta ya kai Dala 510,000, kwatankwacin N193,290,000 ga kowanne daya daga cikin mutum shidan da aka kashe, yayin da kuma za a biya biliyan uku na Sefa ga dukkan mutum 15 din da aka jikkata.
  • Babu kotu ko caji ofis din da aka kai ni —Rahama Sadau
  • Za a yi wa ‘yan sandan da aka kashe a zanga-zangar #EndSARS karin girma
  • Hukuncin wanda aka yanke shi ranar Talata ya biyo bayan zargin zubar da jinin da aka yi a watan Agustan 2012 lokacin da aka fara zanga-zanga a garin Zoghota dake Kudu maso Gabashin kasar kan wani kamfanin hakar ma’adinai na Vale-BSGR da suka zarga da nuna kabilanci a wajen daukar ma’aikata.
    Daga bisani ne dai aka zargi jami’an tsaro da zuwa garin kashe-gari inda suka kashe mutum shida daga cikin masu zanga-zangar, kamar yadda kwafin takardun karar ya nuna.
    To sai dai hukumomin kasar sun musanta aikata laifin, inda suka ce basu take hakkin bil-Adaman da ake zarginsu da yi ba.
    Kotun dai ta yanke hukuncin cewa kasar na da hannu dumu-dumu a take hakkokin masu zanga-zangar ta hanyar azabtar da su da kuma kama wasu ba bisa ka’ida ba.
    Lauyan masu shigar da karar, Pepe Antoine Lama ya ce sun yanke shawarar kai karar ne a kotun ECOWAS saboda bangaren shari’ar kasar bai nuna alamar bincikar lamarin ba.
    A wani labarin kuma, Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta kasar Ginin ta ce hukuncin ya zo mata da ba-zata matuka, tana mai cewa za ta bi duk hanyoyin da suka kamata wajen ganin an yi adalci.
    A watan da ya gabata ne dai aka sake zaben Alpha Conde mai kimanin shekaru 82 a matsayin shugaban kasar a karo na uku, duk kuwa da zanga-zangar da ‘yan adawa ke yi a kan hakan.

    Ron Klain da Joe Biden
     

    Biden Ya Zabi Shugaban Ma’aikatan Fadar White House

    NOVEMBER 12, 2020 AT 1:50:13 PM
     
    ISHAQ ISMA'IL

    Shugaban Amurka mai jiran gado, Joe Biden, ya nada Ron Klain a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar White House.

    Sanarwa da kwamitin karbar mulki na Biden ya fitar a ranar Laraba, ta ce Ron zai jagoranci kula da al’amuran da suka shafi ofishin Shugaban Kasa a matsayinsa na babban mashawarci.
  • Mijin Kamala Harris ya ajiye aikinsa don samun shiga gwamnatin Biden
  • ’Yan matan da ke yunkurin ‘kashe gwamna’ sun gurfana a kotu
  • “Baya ga goyon bayan zababben Shugaban, Mista Klain zai yi aiki don kafa wata tawagar hazikan mutane don taimaka wa Zababben Shugaba Biden da Mataimakiyarsa Kamala Harris su tunkari kalubalen da kasar ke fuskanta”, inji sanarwar.
    Mista Biden ya ce: “Ron ya kasance mai matukar muhimmanci a wurina tsawon shekarun da muka yi aiki tare, musamman yadda muka ceto tattalin arzikin Amurka daga cikin mawuyancin hali a 2009 sannan muka shawo kan wata babbar matsalar lafiyar al’umma a 2014.
    “Zurfin tunaninsa da gogewa a kan aiki da mutane a bangarorin siyasa daban-daban shi ne ainihin abin da nake bukata daga Shugaban Ma’aikata na Fadar White House a yayin da kasarmu ta ke fuskantar kalubale iri-iri”.
    Dangane da nadin nasa, Mista Klain ya ce: “Abin karamci ne a gare ni in yi wa zababben Shugaban Amurka hidima a wannan mukamin kuma amincewarsa da ni ya zamto abin alfahari a gare ni.
    “Ina fata tare da zummar taimaka masa da mataimakiyarsa wajen hada karfi da karfe don yin aiki a White House yayin da muka fuskanci manufofinsu na kawo managarcin sauyi da karshen bambance-bambance a kasarmu”, inji shi.
    Mista Klain Babban Mashawarci ne a Kwamitin yakin neman zaben Mista Biden kuma a baya ya yi wa zababben shugaban kasar ayyuka da dama ciki har sa Shugaban Ma’aikatansa a lokacin da yake Mataimakin Shugaban Kasa.
    Mista Klain ya shahara musamman saboda da rawar da ya taka a matsayin Babban Jami’in Fadar White House mai kula da yaki da cutar Ebola
    Nadin Mista Ron na zuwa ne duk da ki fadin da Shugaba Donald Trump ya yi na amince wa da sakamakon zaben da aka gudanart a ranar 2 ga watan Nuwamba.
     

    Godwin Obaseki, Gwamnan Jihar Edo
     

    An Rantsar Da Gwamna Obaseki A Karo Na Biyu

    NOVEMBER 12, 2020 AT 1:45:30 PM
     
    ISHAQ ISMA’IL MUSA

     

    An rantsar da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shuaaibu a wani sabon wa’adi karo na biyu.
    Lauyar koli ta jihar, Mai Shari’a Esther Edigin ce ta rantsar da Obaseki da mataimakinsa da misalin karfe 12.00 na ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamban 2020.
  • A kan idona sojoji suka kashe Sardauna —Sarkin Mota
  • An kama malami ya yi garkuwa da dalibinsa
  • Daga cikin wadanda suka halarci bikin rantsuwar da aka gudanar a farfajiyar filin wasanni ta Samuel Ogbemudia da ke birnin Benin sun hada da wasu Gwamnonin jam’iyyar PDP ciki har da Nyesom Wike na jihar Ribas, Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato, Ifeanyi Okow ana jihar Delta da kuma Duoye Diri na jihar Bayelsa.
    Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus na cikin wadanda suka albarkaci taron yayin da Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya samu wakilcin wasu manyan jami’an gwamnati.
    Gwamna Obaseki wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP sakamakon hana shi tikitin takara, ya kayar da dan takarar da jam’iyyar APC ta tsayar, Osagie Ize-Iyamu a yayin zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 19 ga watan Satumba.
     

     

    A Kan Idona Sojoji Suka Kashe Sardauna —Sarkin Mota

    NOVEMBER 12, 2020 AT 1:35:51 PM
     
    SAGIRU SALEH KANO

    Rayuwar Sardauna da hakikanin yadda sojoji masu juyin mulki suka kashe shi daga bakin direbansa, Alhaji Ali Sarkin Mota wanda lamarin ya faru a aka idonsa.

     

     Ana Rokon ’Yan Sanda Su Dawo Aiki A Legas

    NOVEMBER 12, 2020 AT 12:56:36 PM
     
    ABUBAKAR MUHAMMAD USMAN DA EUGENE AGHA, LEGAS

    Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, AIG Ahmed Iliyasu mai kuma da shiyya ta 2, ya bukaci jami’an da ke karkashin shiyyar Legas da Ogun su koma bakin aikinsu.

    Ya bayyana haka ne a taron kara wa juna sani da aka yi a Onikan, Jihar Legas, inda ya ce ana bukatar cikakken tsaro kafin da kuma bayan bikin Kirsimeti.
  • #EndSARS: Bata-gari sun sace bindigar AK-47 100 a Legas
  • Muna bukatar N24.8bn na sa mai a motocinmu —‘Yan sanda
  • ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda sun sace makamai
  • #EndSARS: ’Yan sanda sun ba ‘barayin’ makamai wa’adin kwana 7
  • “Dole sai mun sauya dabi’unmu wajen kare mutane ya zama shi ne jigon aikinmu”, cewar Iliyasu.
    Ya roki jami’an rundunar su mance da abin da ya faru lokacin zanga-zangar #EndSARS su koma bakin aikinsu ba tare da damuwa da yadda matasa ke kallon su ba.
    Babban jami’in ya ba wa al’umma tabbacin cewa za a yi gyara a rundunar ta yadda kowa zai iya mu’amala da ita ba tare da tsoro ba.
    Sakamakon kurar da zanga-zangar #EndSARS ta bari a baya a Najeriya, ana sa ran samun sauyi daga bangaren hukumar ta ‘yan sandan.

     

    An Kama Malami Ya Yi Garkuwa Da Dalibinsa

    NOVEMBER 12, 2020 AT 12:31:25 PM
     
    FATIMA MUHAMMAD WADA

    ’Yan Sandan a Jihar Ogun sun damke wani malami, Odugbesan Ayodele Samson, bisa zargin garkuwa da dalibinsa mai shekara takwas.

    Wanda ake zargin ya sace karamin yaron ne ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba ya kuma nemi kudin fansa N200,000 daga mahaifiyar yaron.
  • An yi garkuwa da mashawarcin Gwamnan Sakkwato
  • ’Yan matan da ke yunkurin ‘kashe gwamna’ sun gurfana a kotu
  • Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan Sanda a Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce mahaifiyar yaron, Fatimat Akeeb, ta kai kara cewa an sace danta daga makaranta a yankin Arifanla na Akute.
    Mahaifiyar yaron ta ce daga baya wanda ake zargin ya kira ta a waya ya kuma umurce ta da ta biya N200,000 don a saki danta.
    Oyeyemi ya ce nan take ’yan sanda suka fara binciken har suka kai ga gano maboyar wanda ake zargin.
    “Don kar a cutar da yaron, an yaudari wanda ake zargin tare da biyan wani kaso na fansan sannan daga baya aka cafke shi ya kai ’yan sanda inda ya ajiye yaron wanda aka ceta ba tare da rauni ba”, in ji Oyeyemi.
    Ya ce da aka titsiye wanda ake zargin, ya amsa aikata laifin amma ya ce aikin shaidan ne.
    Kwamishinan ’Yan Sanda Jihar, Edward Awolowo Ajogun, ya ba da umarnin a tura wanda ake zargin zuwa sashin yaki da satar mutane na sashin binciken manyan laifuka don kammala bincike da kuma gurfanar da su a kotu.

    Kamala Harris da Mai gidanta, Doug Emhoff
     

    Mijin Kamala Harris Ya Ajiye Aikinsa Don Samun Shiga Gwamnatin Biden

    NOVEMBER 12, 2020 AT 11:53:56 AM
     
    ISHAQ ISMA’IL MUSA

    Mijin zababbiyar Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka, Kamala Harris, ya ajiye aikinsa a wani Kamfanin Shari’a da nufin samun wuri a fadar gwamnati duk da cewa a baya ya ce ba zai shiga siyasa ba.

    Doug Emhoff wanda babban lauya ne zai bar kamfanin DLA Piper a sa’ilin da za a rantsar da Joe Biden a matsayin Shugaban Amurka a ranar 20 ga watan Janairun 2021.
  • Fursunoni 10 za su tafi jami’a a Kano
  • Sojin Larabawa sun kakkabo jiragen ’yan Houthi a Saudiyya
  • Kwamishinan Lafiyan Jihar Binuwai ya rasu
  • A watan Agusta ne Mista Emhoff ya karbi hutun barin aiki daga DLA Piper yayin da matarsa Kamala ta yanki tikitin takarar mataimakiyar shugaban kasa.
    Yanzu dai Mista Emhoff yana aiki tare da kwamitin karbar mulki na Biden domin kulla dangartakar da za ta samar masa gurbi a gwamnatinsa kamar yadda wani jami’i a kwamitin ya shaida wa kafar watsa labarai ta Fox News.
    Mista Emhoff kwararren lauya ne da ya shekara 25 yana wakilci a gaban kotuna daban-daban musamman a jihar California da sauran sassan Amurka.
    Zai kafa tarihin zama mijin mace ta farko da ta zama mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka.
    A watan jiya ne ya shaida wa mujallar People cewa ba shi da burin zama daga cikin mashawartan mai dakinsa ko da ta yi nasara a zaben da aka gudanar a ranar 2 ga watan Nuwamba.
    “Ni mijinta ne, kuma haka kadai ya wadatar; Tana zagaye da muhimman mutane masu ba ta shawara a siyasance.
    “Ni abokin zamanta ne, ba ta da wani amini da ya zarce ni kuma ni mijinta ne.
    “Saboda haka abin da zan ci gaba da kasancewa a kai ke nan domin ba ta goyon baya”, inji shi.
    A shekarar 2013 ne Emhoff da Kamala suka yi haduwa ta farko, kuma bayan shekara daya suka yi aure a wani dan kwarya-kwaryan biki.
    Suna zaune a wani gidansu da darajarsa ta kai Dala miliyan biyar a unguwar Brentwood da ke Jihar Los Angleles kuma suna da wasu kananan gidaje a birnin Washington da San Francisco.

    ’Yan matan da ke yunkurin ‘kashe gwamna’ sun gurfana a kotu
     

    ’Yan Matan Da Ke Yunkurin ‘Kashe Gwamna’ Sun Gurfana A Kotu

    NOVEMBER 12, 2020 AT 11:41:12 AM
     
    ABUBAKAR MUHAMMAD USMAN

    An gurfanar da wasu ’yan mata biyu gaban kotun bisa zargin yunkurin kashe Gwamnan Adegboyega Oyetola na Jihar Osun.

    Dan sandan mai gabatar da kara John Idoko ya shaida wa Kotun Majistare mai zamanta a Osogbo cewa ’yan matan na daga cikin mutanen da suka fasa babban shagon kasuwanci a garin.
  • An ba wadanda suka saci kayan tallafin Osun sa’o’i 72 su dawo da su
  • An cafke dan sanda da satar waya da kudi a Osun
  • Yadda kungiyar IPOB ta kashe Musulmai da sunan #EndSARS —Okonkwo
  • Hatsarin mota ya salwantar da rayukan fiye da mutum 20 a Osun
  • Ya ce an hada baki da su aka yi yunkurin kashe gwamnan ta hanyar harbi da bindiga da kuma jifa da duwatsu.
    Dan sandan ya ce ’yan matan sun fasa wani babban shagon na Ashiru Ibrahim Olayrmi, suka sace kwamfuta da wayoyin hannu da darajarsu ta kai N3,568,000.00.
    Laifukan a cewarsa, sun saba da kundin laifuka na jihar na 2020 karkashin sashi na 516, 320 (1) da 451, 414 da kuma 390.
    Wadanda ake zargin sun musanta aikata abin da ake tuhumar su da aikatawa sannan lauyansu ya bukaci kotun da ta ba da su beli.
    Amma alkalin kotun, Mai Shari’a Olusegun Ayilara, ya hana tare da umartar a ci gaba da tsare su a kurkuku na Ilesa zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba 2020.

    Fursunoni 10 za su tafi jami’a a Kano
    Jami’ar Karatu Daga Gida ta Najeriya (NOUN)
     

    Fursunoni 10 Za Su Tafi Jami’a A Kano

    NOVEMBER 12, 2020 AT 10:16:47 AM
     
    SAGIR KANO SALEH

    10 daga cikin fursunoni da ke zaman wakafi a Jihar Kano na neman gurbin karatu a Jami’ar Karatu daga Gida ta Najeriya (NOUN).

    Kwanturolan Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya (NPS) na Jihar Kano, Suleiman Suleiman ya ce 17 daga fursunonin da ke jihar na cikin daliban da suka rubuta jarabawar kammala sakandare (WASSCE) ta bana.
  • An tsinci gawar yarinyar da aka yi wa fyade a makabarta
  • Boko Haram: Sojoji na neman mutum 81 ruwa a jallo
  • Ya ce wasu daga cikin masu neman gurbin karatun jami’ar sun riga sun kammala karatun sakandare kafin a kawosu cibiyar.
    Ya kara da cewa masu zaman wakafin da za su yi jarabawa za su yi ne a makarantar ‘ya’yan ma’aikatan NPS da ke gidan yarin Goron Dutse a birnin Kano.
    Don haka ya yi kira ga jama’a da su guji tsangwamar tsoffin fursunonin da suka kammala zaman wakafinsu suka dawo cikin al’umma.
    “Mu daina nuna musu kyama domin kada su koma aika abind a tun farko ya sa aka kai su gidan yari”, inji Suleiman.

    Sojin Larabawa sun kakkabo jiragen ’yan Houthi a Saudiyya
    Kakakin Rundunar Kawancen Kasashen Larabawa, Kanar Turki Al-Maliki
     

    Sojin Larabawa Sun Kakkabo Jiragen ’Yan Houthi A Saudiyya

    NOVEMBER 12, 2020 AT 9:55:36 AM
     
    SAGIR KANO SALEH

    Rundunar kawancen kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta sun baro jiragen yaki marasa matuka na ’yan tawayen Houthi na kasar Yemen.

    Rundunar ta kama jiragen ne makare da ababen fashewa a yankin Kudancin Saudiyya ta kuma ta tarwatsa su.
  • Bam ya tashi a wata makabarta a Saudiyya
  • Firaministan Bahrain ya rasu bayan shafe shekaru 49 a kan mulki
  • Kakakin Rundunar, Kanar Turki Al-Maliki ya ce: “A safiyar Alhamis rundunar ta cafke jirage mara matuki dauke da makamai da ’yan tawayen Houthi suka kai wa fararen hula hari da su a yankin Kudanci”.
    Harin na zuwa ne bayan a ranar Laraba sojin ruwan rundunar kawancen sun tarwatsa wasu jiragen ruwan mayakan Houthi makare da ababen fashewa a kan tekun Bahar Maliya.
    A baya-bayan nan ’yan tawayen na Yemen sun tsananta kai hare-hare a makwabtan kasar sabanin dokokin kasashen duniya da ma na cikin gidan 

    Advertisement

    Loading...

    Link socials

    Matches

    Loading...